Hausa

An Fara Shirye Shiryen Auren Rukayya Dawayya Da Afakallah Shugaban Tace Finafinan Hausa

An Fara Shirye Shiryen Auren Rukayya Dawayya Da Afakallah Shugaban Tace Finafinan Hausa

Isma’ila Na’Abba Afakallahu na shirin auren tsohuwar jarumar Kannywood, Rukayya Dawayya kamar yadda alamu su ka nuna.

Afakallah shi ne shugaban hukumar tantance fina-finai ta Jihar Kano kamar yadda Gwamnan Jihar, Abdullahi Umar Ganduje ya nada shi.

A lokacin, gwamnan ya ce ya nada shi ne don ganin ya zakulo daya daga cikin ‘yan industirin wanda zai iya kawo ci gaba wurin kayan aiki, horar da darektoci da jarumai da sauransu.

Sai dai a cikin makon nan rade-radi yayi yawa dangane da batun aurensu da jaruma Rukayya Dawayya.

An samu tabbaci dangane da hakan ne ta wata wallafa da tayi a shafinta na Instagram a ranar Juma’a 15 ga watan

Yulin 2022.

Kamar yadda ta sanya a shafin nata mai suna DawayyaRukayya85, ta ce shi din amsa ne ga addu’ar da ta dade tana yi tare da kiransa masoyinta na gaskiya.

Kamar yadda ta wallafa hotonsa ta yi tsokaci a kasa inda tace:

“Samun masoyin gaskiya a wannan zamanin da rashin gaskiya tayi yawa sai karfin addu’a. Alhamdulillah ya Rabbi, lakal hamdu wash shukur.

“Allah na gode maka da ka amsa addu’a ta. Khairun nas man yan fa un nass.”

Nan da nan jarumai da sauran masu mata fatan alkhairi su ka dinga zuba mata addu’o’i da fatan alkhairi a bangaren tsokaci.

Muna fatan Ubangiji ya tabbatar musu da alkhairi. Ameen.

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button