Hausa

Wani Mutum Ya Suma A Lokacin Da Ya Gano Gidan Da Yake Haya Har Shekara Goma Na Matar Shi Ne

Wani Mutum Ya Suma A Lokacin Da Ya Gano Gidan Da Yake Haya Har Shekara Goma Na Matar Shi Ne

Wani mai matakaitan shekaru ya fadi ya suma bayan da ya gano cewa gidan yake haya na tsawon shekaru goma (10) mallakar matar da yake aure da ita ne, kamar yanda wata jarida mai suna Occupgh.com ta labarta a jiya Assabar.

Mutumin wanda har yanzu ba’a bayyana sunan sa ba, ya yanke jiki ya fadi saboda jin wannan labarin mai gir-giza hankali.

Wani mutum mai amfani da shafin sada zumunta na Facebook shine ya bayyana wannan mummunan labarin kamar yanda ya wallafa a shafin shi a kasa;

Wani mutum wanda ya biya kudin hayar gida na shekara goma (10) ga matar shi, wanda bai san da hakan ba sai da wani mai tsegumi ya labarta masa abinda ke faruwa.

Mutumin ya kalubalanci matar tasa akan gaskiyar abinda yaji, wanda bayan dogon rikici matar ta fada masa gaskiyar maganar, wanda ya sanya ya fadi tare da sumu tun satin da ya gabata.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button